Dangantakar Afurka Da Kasashen Yammaci
October 25, 2004Akwai dai banbancin ra’ayi tsakanin masana a game da wannan batu. Misali wani masanin al’amuran afurka daga jami’ar Florida ta kasar Amurka Goran Hyden, a cikin wani bayanin da yayi yayi nuni da cewar ko shakka babu a game da cewar mulkin mallaka yayi mummunan barna ga al’umar Afurka, wajen jirkita tsare-tsarensu na rayuwa da zamantakewa da kuma hanyoyi na noma da kere-kere da makamantansu, amma a daya hannun Turawan mulkin mallaka sun taimaka wajen kyautata ma’amallar nahiyar Afurka da sauran sassa na duniya. Jami’in ya kara da cewar:
"Ko shakka bau daulolin mulkin mallaka sun yi babban tasiri akan tsare-tsaren rayuwa da zamantakewar jama’a tsawon shekaru da dama da suka yi suna mulkar yankunan nahiyar Afurka. Amma hakan baya ma’anar cewar al’umar Afurka sun yi watsi ne kwata-kwata da dukkan muhimman bangarorinsu na rayuwa ta yau da kullum. Kasashen Afurka da dama da suka samu ‚yancin kansu a cikin shekarun 1960 sun yi bakin kokarinsu wajen sake raya wadannan tsare-tsare, amma kuma a lokaci guda sun kokarta wajen cudanyya wadannan tsare-tsare da abubuwan da suka gada daga ‚yan mulkin mallaka na Faransa, Birtaniya, Belgium da Spain."
Bayan kawo karshen mulkin mallaka, kasashen Afurka sun bi tsarin mulki ne na gwamnatin tsakiya kuma gwamnatocin da aka nada a wawware sun yi bakin kokarinsu wajen hadin kan al'umar kasa da aka rarraba su a tsakanin iyakokin da aka shata, ba kuwa tare da wata takamaimiyar masaniya a game da yadda zasu billo wa lamarin ba. Goran Hyden ya kara da cewar:
"Ita Afurka tun fil-azal bata da wani tsari na wata kasa daya al’uma daya, wanda za a iya dori akansa bayan samun ‚yancin kai, in ka kebe Habasha da Afurka ta Kudu bai daya. Dukkan kasashen kirkirosu aka yi, ba wani ci gaba ne na tarihi ya samu har suka tsaya kan kafafuwansu sannu a hankali ba."
Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda ake fama da tafiyar hawainiya wajen sabunta al’amuran Afurka da kuma dora ta kan wata sahihiyar hanya ta demokradiyya. Abu daya da zai taimaka a fita daga wannan mawuyacin hali na kaka-nika-yi shi ne a rika ba da la’akari da ainifin al’adu da tsare-tsaren rayuwa dake da tushensu a wannan nahiya a dukkan manufofin da za a gabatar, a maimakon da a rika yin koyi da al’adu da kuma salon rayuwa na kasashen yammaci. Masu iya magana dai su kan ce: Kayan aro baya ado.