1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da China mai sarkakiya

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
June 20, 2023

Jamus da China sun jima suna duba hanyoyin kulla dangantaka, amma batun ya koma sukan juna. Yanzu dai ana sa ran wata tattaunawa a tsakanin kasashen karo na bakwai.

https://p.dw.com/p/4SqIQ
Firaministan China da Shugaban gwamnatin Jamus
Firaministan China Li Qiang da shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

"Mu yi aiki mai dorewa tare" Wannan shi ne taken dangantakar da Jamus da China ke son kullawa a tsakaninsu. Ana sa ran wakilan gwamnatocin kasashen biyu za su tattauna kan wannan batu, yayin ziyarar firaministan China Li Qiang tare da tawagarsa a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a wannan mako. Sai dai kuma a fili yake dangantaka tsakanin Beijing da Berlin na kara tsami, idan aka yi la'akari da tattaunawar da ta gudana tsakanin ministan tsaro Jamus Boris Pistorius da takwaransa na China Li Shangfu, a gefen taro kan al'amuran tsaro a Singapore. Pistorius din dai ya bukaci a kawo karshen sanannen tsarin horo tsakanin sojojin sama na China da kuma tsofaffin matuka jiragen yakin Jamus nan take. Hakan  ya sanya Thorsten Benner na cibiyar nazarin tsare-tsaren gwamnati ta Jamus GPPI da ke Berlin, tunanin cewa ya kamata a farka daga bacci.

Ko dai kokarin dora hannayenta kan fasahohin Jamus ko kuma alaka mai karfi da ke tsakaninta da Moscow duk kuwa da cewa Rasha ta mamaye Ukraine, karuwar barazana a yankin Taiwan da kuma kokarin danniya ga 'yan kabilar Uyghur marasa rinjaye a Chinan, duka wadannan na kara iza wutar rashin jituwa a tsakanin Jamus da China. Haka kuma kokarin zama kan gaba wajen fada a ji tsakanin Beijing da Amurka ma ba zai rasa nasaba da rashin jituwar tasu ba. 

Firaministan China da Shugaban gwamnatin Jamus
Hoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP

Duk da haka dai, China na zaman babbar abokiyar huldar kasuwanci ga Jamus shekaru bakwai a jere. A shekara ta 2022, an yi hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kudinsu ya kai kusan Euro biliyan uku. Alakar da ke tsakanin kasashen biyu mai girma ce, duk wata sarkakiya da huldar kasashen biyu ke da ita dai, a bayyane yake an ambaci China a hukumance a matsayin abokiyar hulda kana abokiyar hamayya a lokaci guda. 

A baya, Berlin ta bai wa bangaren huldar muhimmanci. Tattaunawar da ke gudana tun a shekara ta 2011, ta shaidar da hakan domin kuwa ana irinta ne da abokan hulda na kusa. A 2014, dangantakar Jamus da China ta daga zuwa "kyakkyawar alakar tsare-tsare". 
Sai dai tuni yanayin ya sauya a Berlin da ma sauran kasashen Turai, inda dangantakar ta koma hamayya. Wannan dai zai shafi tattaunawar gwamnatocin biyu karo na bakwai, a ganin mamba a cibiyar Merics da ke nazarin harkokin siyasar China a Berlin.