1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Tunusiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2017

Yayin ziyarar Angela Merkel a Tunusiya kasashen biyu sun amince da wasu matakai da za su taimaka wajen gaggauta mayar da masu neman mafaka a Jamus din daga Tunusiyan da takaddunsu ba su samu shiga ba.

https://p.dw.com/p/2YctJ
Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hoto: Reuters/Z. Souissi

Shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ce ta bayana hakan jim kadan byan ganawarta da shugaban Tunusiyan Beji Caid Essebsi a Tunis babban birnin kasar ta Tunusiya. A cewar Merkel din wadda ta fara wata ziyarar aiki a Tunusiyan, nan gaba za a rinka baje fasfo din masu neman mafakar da basu samu nasara ba cikin mako guda, kana Jamus za ta tallafa musu in sun koma gida fiye da yadda ta ke taimakon su a baya. A nasa bangaren Essebsi ya bayyana yarjejeniyar da suka cimma da wata kyakkyawar matsaya. Matakan da Jamus din ke son dauka kan masu neman mafaka daga Tunusiya dai na zuwa ne biyo bayan harin ta'addancin da wani dan Tunusiyan da ba a amince da bukatunsa na neman mafaka ba ya kai a kasuwar Kirsimeti da ke Berlin fadar gwamnatin Jamus din a watan Disambar bara. Harin da aka danganta shi da tsaikon da aka samu na samun takaddunsa daga mahukuntan Tunusiyan, wadanda za su bayar da damar mai da shi gida.