Nijar: Karfafa dangantaka da makwabta
September 30, 2021Tuni dai wasu al'ummar Jamhuriyar ta Nijar suka soma tofa albarkacin bakinsu, dangane da yadda kasar ke karfafa huldarta da kasashen Larabawa makwabtanta tun bayan hawan Shugaba Mohamed Bazoum karagar mulki. Bayan ganawar tawagar Aljeriyan da Shugaba Bazoum a fadarsa, ministan cikin gida na kasar ta Aljeriya Kamel Beldjoud ya bayyana cewa ziyarar tasu na da burin aiwatar da yarjeniyoyin da kasashen biyu suka cimma a ziyarar da Shugaban Nijar din ya kai a Aljeriyan a watan Yulin wannan shekara.
A nata bangare tawagar jami'an gwamnatin Libiya ta isa Nijar a karkashin jagorancin firaministan rikon kwarya na kasar Abdul Hamid Dbeibeh. Firamnistan na Libiya dai ya share sa'o'i yana ganawa da Shugaba Bazoum a fadarsa, inda Nijar ta bayyana bukatar hadin kai tsakaninta da kasar ta Libiya wajen shawo kan matsalolin tsaron da take fuskanta. Tu dai bayan hawan Shugaba Bazouma kan karagar mulki watanni shidan da suka gabata, Nijar da ke da hulda ta kut da kut da makwabtanta, take neman karfafa dangantakarta da kasashen Larabawa da ke makwabtaka da itan. Yanzu haka dai tawagar ta jami'an gwamnatocin kasashen na Libiya da Aljeriya, na ci gaba da ziyarar tasu tare da ganawa da hukumomi dabam-dabam na Jamhuriyar ta Nijar.