Daniel Galvan ya shiga hannun mahukuntan Spain
August 5, 2013'Yan sanda a ƙasar Spain sun kame mutumin nan mai lalata da ƙananan yara wanda sarkin Morocco, Mohammed na shidda ya janye afuwar da ya yi masa bayan da matakin ya janyo zanga-zanga a ƙasar.
Daniel Galvan mai shekaru 64 na haihuwa wanda kotu ta same shi da laifin yiwa yara 11, 'yan shekaru huɗu zuwa 15 fyaɗe, aka kuma yanke mishi hukuncin ɗauri na shekaru 30 a kurkuku ya shiga hanun jami'an tsaron Spain ne a garin Murcia da ke yankin kudu maso gabashin Spain, bisa bayanan da mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan ƙasar ya bayar
Ministocin shari'an Morocco da Spain sun tattauna wannan batu ta wayar tarho inda suka yi alƙawarin yin hadin kai dan ɗaukar mataki na bai ɗaya dangane da wannan matsala.
To sai dai ana ganin zai yi wahala a ce Spain ta miƙa Daniel Galvan a yi masa shari'a a wata ƙasa ta daban kasancewar bata yadda da miƙa 'yan ƙasarta haka nan.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman