Darajar Euro na nan daram
June 2, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kare martabar kuɗin Euro ta na mai baiyana shi da cewa yana da ƙarfi da daraja.
Merkel wadda ta baiyana haka a lokacin ziyararta a Singapore ta shaidawa taron masana harkokin tattalin arziki cewa nahiyar Turai ba ta fuskantar wata matsala da kuɗin na euro, illa dai kawai matsalar bashi wanda kuma za'a shawo kansa. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma yi kiran samar da ƙarin haɗin kai a tsakani ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin na euro. Jawabin na Merkel ya zo ne a daidai lokacin da hukumar dake sa ido kan harkokin kuɗaɗe ta sassauta bashin da ake bin ƙasar Girka. A shekarar da ta gabata Girka ta karɓi bashin euro biliyan 110 na tallafi daga ƙungiyar Tarayyar Turai da asusun bada lamuni na duniya IMF domin ceto tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa, ta na kuma tattauna karɓar wani bashin na euro biliyan 65 a nan gaba.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu