1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darajar kudin Ruble na Rasha ta hau

Abdourahamane Hassane
March 23, 2022

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya ce ba zai sake karbar kudin Yuro ba ko Dala, na cinikin da Turai take yi wajen sayo iskan gas daga Rashar.

https://p.dw.com/p/48x77
Russland l Russische Währung - Rubel l Bezahlen, Einkauf
Hoto: Alexey Malgavko/REUTERS

Putin ya ce, ya bai wa kasashen na Turai wa'adin mako guda, su samar da wani  tsarin da za su biyan kudin gas din. da kudin Ruble na Rasha a maimakon kudin Yuro ko Dala da suke biya da shi. Shugaban na Rasha ya bukaci babban bankin Turai da gwamnati da su kafa wani sabon tsari wanda dole ya ƙunshi sayan Ruble a kasuwannin musayar kudi.Wannan sanarwar dai ta yi tasiri nan da nan a kan kudin kasar na Rasha, wanda ya tashi a kasuwannin hannayen jari fiye da kudin Yuro da Dala. Fadar shugaban kasar Ukraine ta yi Allah wadai da yakin tattalin arziki da Moscow take yi don karfafa kudinta na Ruble.