1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dari-darin EU na tura 'yan sanda Ukraine

Suleiman BabayoFebruary 20, 2015

Shugaba Poroshenko na Ukraine ya bukaci kungiyar kasashen Tarayyar Turai ta tura da 'yan sanda a yankin da ke fama da rikici. Sai dai EU ta nuna shakku kan shirin.

https://p.dw.com/p/1EfDJ
Hoto: AFP/Getty Images/S. Supinsky

Tun lokacin da garin Debaltseve mai muhimmanci ya fada hannu 'yan aware masu goyon bayan Rasha, Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya gabatar da bukatar ganin Kungiyar Kasashen Turai ta tura jami'an 'yan sanda zuwa gabashin kasar, domin saka ido kan shirin yarjejeniyar tsagaita wuta. Shugaba Poroshenko ya bukaci 'yan sanda na kasashen Turai su samu izinin Majalisar Dinkin Duniya domin samun damar shiga yankunan gabashin kasar da ya dace ana aiki da shirin tsagaita wuta.

Tuni kungiyar Tarayyar Turai ta nuna dari-dari kamar yadda babbar jami'ar kula da harkokin kasashen ketare na EU Federica Mogherini ta nunar saboda akwai kungiyar tsaro da hadin kan Turai da ke saka ido.Kasashen Ukraine, da Rasha, da Jamus da kuma Faransa suka amince da wannan shiri. Akwai 'yan kungiyar kimanin 450 da suka hada da Amirkawa da ke lura da lamura tun lokacin da Rasha ta mayar da yankin Kirimiya karkashin ikonta.

Sojojin Ukraine sun kasa shre wa shugaba poroschenko hawaye
Hoto: reuters

Maciej Popowski babban jami'in difolomasiya na kungiyar Tarayyar Turai bayyana babban abin da suka saka a gaba ya yi, inda ya ce "Abin da muke baiwa fifiko shi ne aiwatar da yarjejeniyar birnin Minsk."

Yarjejeniyar birnin Minsk ta tanadi cewa mambobin kungiyar tsaro da hadin Turai, OSCE, su saka ido kan yankin da ke zama fagen daga kimanin kilomita 50 zuwa 100 a gabashin kasar ta Ukraine, domin tabbatar da mutunta yarjejeniyar tsakanin gwamnati da 'yan awaren gabashin kasar. Jami'an difolomasiya na kungiyar Tarayyar Turai da ke birnin Brussel sun nunar da cewa zai yi wuya dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD daga kasashe za su iya tabbatar da shiga tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.