1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Daruruwan mahajjata ne suka rasa rayukansu a bana

June 20, 2024

Sama da mahajjata mutum dubu guda ne aka tabbatar da cewa suka rasu yayin aikin Hajjin bana, saboda tsananin yanayi na zafi da aka gani a kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4hKWL
Yadda tsananin zafi ya yi ajalin mutane a Saudiyya
Yadda tsananin zafi ya yi ajalin mutane a SaudiyyaHoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Aikin Hajjin dai na kunshe da ayyukan ibada na tafiya a kafa na wasu sa'o'i a kasar da alkaluman zafi ya kai maki 51.8 a ma'aunin Celcius a wannan mako.

Aikin na Hajji dai na daga cikin manyan taruka da ake yi a duniya inda sama da mutum miliyan 1.8 suka gudanar da shi a wannan shekara.

Daga cikin wannan adadi dai baki daga wajen Saudiyyar mutum miliyan daya da dubu 600 ne.

Hukumomi a Saudiyyar sun ce an kai rahoton sama da mutum 2,700 da suka yi fama da matsaloli masu nasaba da tsananin zafi a ranar Lahadi kadai.