An daure mai hada ma IS bidiyo
July 31, 2022Wata kotu a Amirka, ta yanke wa wani Mohammed Khalifa hukuncin daurin rai-da-rai, bayan samun shi da laifin hannu a hada wa Kungiyar IS bidiyo na yadda aka yi wa wasu Amirkawa kisan gilla. Bincike ya tantance muryoyinsa a faya-fayen bidiyon farfaganda dabam-dabam da Kungiyar IS da ke fafutukar kafa daular musulunci a Iraki ta fitar a shekarun 2014 da 2017.
Khalifa mai shekaru talatin da tara da haihuwa ne ya fassara sautin bidiyon daga Larabci zuwa Turancin Ingilishi, a yayin da mayakan IS suke fille kan wasu Turawa a cikin bidiyon, daga cikin tarin mutanen da suka hallaka, har da 'yan jaridan Amirka biyu da suka hada da James Foley da Steven Sotloff.
Khalifa haifafen kasar Saudiyya ne amma kuma yana amfani da fasfon din sa na kasar Kanada inda ya nemi mafaka. A shekarar 2019 aka kama shi a yayin wani hari da Amirka ta kaddamar ta sama a kasar Siriya kafin a maida shi kasar Amirka inda aka gudanar da shari'ar da kuma zartas da hukuncin.