Jimamin hadarin Ukraine a taron Davos
January 18, 2023Kasancewa wannan hatsari na jirgi mai saukar ungulu ya faru ne a Ukraine a dai-dai lokacin da kasar ke tsakiyar yaki, ya sa mutuwar jami'an gwamnatin ya dauki hankalin matuka, abin da ma yasa shugaban taron na Davos ya nemi a yi shiru na minti guda don girmama wa mamatan. Uwargidan Shugaban kasar Ukraine Olena Zelenska kan hatsarin.
" Yau wata rana ce mai wahala ga dukkanmu, a yau muna da sabbin asara, shi ya sa nake kara godiya da cewa kuna tare da mu. Na gode da goyon bayan Ukraine da jama'armu, kuma na tabbata, saboda goyon bayan kyawawan dabi'unmu ne kuke yin hakan. Kuma wannan shi ne ainihin abu mafi mahimmanci a ganina, wanda ya kamata a yi a yanzu, lokacin da irin wannan mummunan yaki na Rasha a kan kasarmu da jama'armu".
A nasa jawabin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi karin haske kan karin tallafin kudi da kayan yaki ga Ukraine. Ya nuna wa taron na Davos irin kokarin Jamus da kuma kan yakin da kuma sake gina kasar Ukraine.
Bayan jimamin abin da ya faru a kasar Ukraine, wani abu da ya dau hankalin taron na yau shi ne batun gurbata mahalli Wanda yanzu ke neman kassara tattalin arzikin duniya. Inda sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya fadawa taron cewa:
"Muna kan fafatawa da matsalar yanayi, ko wane mako yana kawo sabon labari mai ban tsoro game da yanayi, iskar gas mai gurbata muhalli yana cikin matakai mafiya girma, kuma yana karuwa. Alkawarin kayyade yanayin zafi na duniya zuwa digiri 1.5 yana kusan habaka cikin hayaki."
Guterres ya ce, yin hulda mai ma'ana kan yanayi da kasuwanci da fasaha tsakanin Amirka da China da ke yin sabanin ra'ayi kan batutuwan da suka hada da ciniki da 'yancin dan Adam yana da matukar muhimmanci don hana yin karo da juna, a kokarin da ake yi na rage dumamar duniya da bunkasa tattalin arziki.