1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dawo da dokar ta baci a Tunusiya

Salissou BoukariNovember 25, 2015

Bayan wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an da ke tsaron lafiyar sa, shugaban kasar Tunusiya Beji Caïd El-Sebsi ya sake ayyana dokar ta baci a kaf fadin kasar.

https://p.dw.com/p/1HC7h
Hoto: Getty Images/AFP/F. Belaid

A yammacin Talata shugaban kasar Tunisiya ya sake dawo da dokar ta baci a wannan kasa bayan wani hari da ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an da ke tsaron lafiyarsa 12 tare kuma da jikkata wasu 20 sakamakon harin da aka kai kan motar safa da suke ciki a tsakiyar birnin na Tunis.

A cikin wani jawabi da ya yi Shugaban kasar ta Tunusiya Béji Caïd El-Sebsi, ya sanar da sake dawo da dokar ta baci a kaf fadin kasar, tare kuma da saka dokar hana fita da dare a wannan dare da ta fara aiki daga karfe tara na dare zuwa karfe biyar na asuba, kuma shugaban ya soke wata ziyara da ta kamata ya yi zuwa kasar Switzerland.

A farkon watan Oktoba da ya gabata aka dage dokar ta baci a kasar ta Tunusiya bayan wani harin da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 38 wanda kungiyar IS ta dauki alhaki.