Desmond Tutu ya rasu a shekara 90
Shi ne Bischof Angalika na bakar fata na farko a Johannesburg, ya zama Archbishop a Cape Town. Ya yi fafutuka tare da Mandela kan wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Ya rasu watanni biyu bayan cika shekara 90 a duniya.
Tsufa cikin izza
An haifi Tutu a shekarar 1931 a yankin Klerksdorp mai arzikin ma'adinai, daga bisani ya zama malamin makaranta. Ya ajiye aiki saboda nuna wariya ga dalibai bakake da gwamnatin wariyar launin fata ke yi. Ya koma karatun addini, inda ya zama Bishop din Angalikan na farko bakar fata a Johannesburg. A wannan hoton, yana bikin cika shekaru 86 a birnin Cape Town, yayin bayani kan mutuwa cikin izza.
Abokin tafiyar Nelson Mandela
Al'ummar Afirka ta Kudu na alakanta rayuwar Desmond Tutu da ta Nelson Mandela. Kwararru da dama a kasar na ganin Mandela ne ya yi fafutuka kan siyasa yayin da Tutu ya yi ga mutane. A gare su, ba zai yiwu a samu Afirka ta Kudu ba tare da muryar Tutu ba. Muryar da ke yin amo tsawon shekaru 90.
Jagoran Hukumar Tantance Gaskiya da Sasantawa
Bayan kammala rikicin wariyar launin fata, Mandela ya nemi Tutu ya jagoranci Hukumar Tantance Gaskiya da Sasanta Al'umma da aka dorawa alhakin tantance laifukan da aka aikata a rikicin. Tutu da hukumar na son yin adalci ga wadanda rikicin ya rutsa da su da yafiya tare da yin kiran a sasanta. Mutane 2000 sun bayar da shaida a bainar jama'a. Tutu ya halarci bayar da shaidun kimanin mutane 1500.
Ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, saboda yaki da wariya
Fafutukarsa ta yaki da wariyar launin fata ba tare da zub da jini ba, ta sa Desmond Tutu samun karramawa daga al'ummomin kasa da kasa. Yayin da 'yan fafutuka kamar Nelson Mandela ke kurkuku, ya jagoranci gangamin yaki da wariya. Ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a 1984. Cikin hoto Egil Aarvik daga kwamitin bayar da kyautar Nobel a birnin Oslo, yayin bai wa Tutu kyautar zaman lafiyar ta Nobel.
Tunawa ta har abada
Tare da sauran 'yan Afirka ta Kudu da suka samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, a shekarar 2005 an kafa mutum-mutumin Desmond Tutu a dandalin Nobel da ke tsakiyar birnin Cape Town. Mutum-mutumin mutane hudu don tunawa ta din-din-din. Albert Luthuli da ya lashe kyautar a 1960 da Desmond Tutu da ya karba a 1984, sai kuma F.W. de Klerk da Nelson Mandela da suka lashe kyautar tare a shekara ta 1993.
Malamin addini da ke da hulda da al'ummomin kasa da kasa
Archbishop Desmond Tutu shugaban kyawawan dabi'u a Afirka ta Kudu, jagoran gangamin kare hakkin dan Adam da yaki da nuna wariya. Daga wajensa aka samu kalaman "kasarmu, kasar bakan-gizo ce." Bai kasance babban abokin Mandela kawai ba, ana girmama shi a duniya baki daya har ma da Dalai Lama. Cikin hoto: Malaman addinan su biyu yayin taron zaman lafiya na Hiroshima a shekara ta 2006.
Tutu na tare da Afirka ta Kudu
Yayin da Afirka ta Kudu ta karbi bakoncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a 2010, ba a bar Desmond Tutu a baya ba. Ya nuna kansa a matsayin dan kishin kasa. Hoton Tutu cikin farin ciki yayin bude gasar gabanin wasan Afirka ta Kudu da Mexico, a ranar 11 ga watan Yunin 2010 a birnin Johannesburg. Abin da ya rage algaitar vuvuzela, wacce bisa ga al'ada magoya bayan Afirka ta Kudu ke busawa.
Alamun kyawawan dabi'u
Nelson Mandela ya saka Desmond Tutu cikin kungiyarsa ta "The Elders," da ya samar a 2010. Kungiyar ta kasa da kasa na aiki tare kan mutumtawa da kare hakkin dan Adam. Tun farkon kafa ta, kungiyar ta kunshi fitattun mutane na kasa da kasa.
Tutu: Mutumin iyalinsa
Leah Nomalizo Tutu mata ga Desmond Tutu na tare da shi tun farkon fafutukar yaki da wariyar launin fata, ma'auratan da ke kaunar junansu. 'Yar fafutukar ta auri Desmond Tutu ranar biyu ga watan Yulin 1955, kafin ya ajiye malamin makaranta ya koma na addini. Suna da yara hudu da jikoki tara. Sun kafa kungiyar hadin gwiwa ta sasantawa da sulhunta rikici. Barka da zagayowar ranar haihuwa "Arch" Tutu!