010212 Deutsche Welle Auftritt
February 2, 2012Tare da gabatar da wani sabon fasali a yanar gizo ƙarƙashin sabon adreshinta www.dw.de da kuma sabuwar alamarta haɗe da canje-canje ga shirye-shiryenta na telebijin Deutsche Welle za ta buɗe wani sabon babi ga matsayinta a gasar kafofin yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa tun daga ranar shida ga watan Fabrairu.
Sabon shafin na yanar gizo zai ƙunshi dukkan ɓangarorin da DW ke yaɗa labarai da sauran shirye-shiryenta a dunƙule, kama daga rubutattun rahotanni zuwa bidiyo da rediyo. Wannan adreshin dw.de tamkar wata madogara ce ta samun sahihan labarai daga Jamus kuma masu ma'ana a cikin harsuna 30. Sabon launin da aka tanada da kuma zanen da ya dace da tafiyar zamani zasu ba wa shafin wata sabuwar fuska mai ƙayatarwa, in ji shugaba DW Erik Bettermann.
"A ganina sabunta fasalin ayyukanmu daidai da yankunan da muke watsa shirye-shiryenmu a cikinsu wani sabon yunƙuri ne da nike fata zai cimma nasara tare da ƙara duƙufa akan ainihin buƙatun mutane a waɗannan yankuna."
A matsayin ƙwararriyar masaniya daga Jamus DW ta ɗauki alhakin bitar abubuwan dake faruwa da kuma irin ci gaban da ake samu tare da tantancewa domin gabatar da su ga abokan hulɗarta. Da wannan azamar sabon matakin na DW zai riƙa gabatar da shirye-shiryensa daga dukkan ɓangarori na yaɗa labarai.
Sabon shafin yanar gizon na DW ya ƙunshi rahotanni ne da aka rattaɓa daidai da batutuwan da suka shafa domin dacewa da buƙatun masu amfani da shafin. Tsarin shimfiɗar shafin na ba da damar shigar da ƙarin hututa da bidiyo da kuma cikakkun rahotanni akan harkokin yau da kullum a cikin harsuna da ɓangarorin yaɗa labarai dabam-dabam.
Alama ta bai ɗaya ga kafofin DW
Tun daga yanzu za a shigar da cibiyar yaɗa labarai ta DW kai tsaye a shafin dw.de ta yadda mai amfani da shafi zai samu kafar kallon bidiyo da sauraren rahotanni da kutsawa taskar hotuna da suka shafi harkokin yau da kullum kai tsaye.
A wani bayani da yayi dangane da wannan sabon fasali da DW ta ɗauka, Philipp Schäfer daga sashen hulɗar ciniki na DW ƙara wa yayi da cewar:
"Wannan sabon fasalin yana ɗaukar hankali sosai da sosai saboda tamkar wata shaida ce mai yin nuni da ainihin yadda aka san ƙirar Jamus. Shirye-shiryen DW sun dogara ne akan tsake gaskiya ba tare da nuna son kai ba kamar dai yadda su kansu masu sauraron tashar suka saba faɗa."
Sabbin shirye-shirye na telebijin DW
A ɓangaren telebijin ma tun daga yanzu DW zata gabatar da sabbin shirye-shiryenta ne a cikin wata sabuwar suffa. Za a dai ci gaba da gabatar da muhimman labarai na duniya kamar yadda aka saba. A baya ga haka DW zata gabatar da shirye-shirye da rahotanni da shirye-shirye na bincike da aka yarfe gumi wajen samar da su.
A karon farko a cikin tarihin DW an tanadar da tsarin kiɗa bai ɗaya tsakanin gidahen rediyo da telebijin domin zama wata shaida ga sabon fasalin da tashar da ɗauka. Jigon kiɗan dai shi ne kiɗe-kiɗen da za a riƙa amfani da su wajen buɗe shirye-shiryen rediyo da telebijin. Misali wannan kiɗan da aka zayyana domin gabatar da shirye-shirye na harkokin yau.
Duk mai tambaya ko wata shawara da zai bayar sai ya rubuta zuwa ga [email protected]. Masu sauraro ku ne zaku iya nuna mana ko wannan sabon fasalin na DW ya gamsar da ku. Za kuma mu yi farin cikin samun hotuna da zane ko kuma sassaƙen sabuwar alamar ta DW daga gare ku. An tanadar da na'urar iPads guda uku da Nokia Lumia 710 Smartphone 20 ga wanda suka ci nasarar gasar ta hanyar refil.
Mawallafi: Birgit Görtz/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal