Dokar bai daya ta shawo kan matsaloli a Turai
September 19, 2022Talla
A karkashin sabuwar dokar, ana iya tilasta wa kamfanonin Turai su bada fifiko wajen samar da muhimman kayayyakin da ake bukata da kuma tara su ko kuma su fuskanci tara.
Mataimakiyar shugabar hukumar tarayyar Turan Margrethe Vestager ta ce suna bukatar samar da yanayi da zai basu damar mayar da martani da daukar matakin bai daya cikin gaggawa.
Shawarar dokar gaggawa a kasashen masu amfani da kudin bai daya zai baiwa hukumar damar umartar kasashe su sauya fasalin kayayyakin da suke samarwa domin bada fifiko ga kayayyakin da ake fuskantar matsalar samuwarsu a kasuwanni.