Dokar girka kafofin sadarwa masu zaman kansu a Guine Konakri
August 23, 2005Bayan shekaru 47, da samun yancin kai, daga turawan mulkin mallaka, da kuma haramcin girka kafofin sadarwa masu zaman kansu, a karshe dai gwamnatin kasar Guinee Conakry, ta gano cewa, riga zamani a saki a huta, ta hanyar dage wannan doka.
Daga samun yancin kan kasar a shekara ta 1958 ya zuwa yanzu,gidajen rediyo da talbajan na gwamnati kadai, ke cin karan su babu babbaka, tare bada labaran da su ka gadama na gaskiya ko karya, baban burin da yan jaridar kasar su ka sa gaba, shine na wasa jami´an gwamnati, da mukaraban su.
A shekara ta 1992 a lokacin da iskan demokradiya ya buga a kasashen Afrika, Shugaba Lansana Kwante, ya bada izinin kafa mujjalu, masu zaman kansu, tare da gidanya sharrudan da ke dabaye aikin jarida.
Shekaru da dama al´ummomin Guinee, na bukatar samun rediyoyi da gidajen telvajan masu zaman kansu, ba tare da cimma biyan bukata ba.
Saidai, a wani mataki na ba zata ,taron majalisar ministocin da ya gabata, ya yanke shawara kirkiro dokar bada wannan izini.
Sanarwar da fadar gwamnati ta bayana, na nuni cewa, daga yanzu dukan dan kasar Guinee Conakry, mai bukata na da yancin buda gidan redio ko talavajan.
Jama´a daban daban a kasar sun fara huruci a kann dokar.
Shugaban hukumar tsara ayyukan sadarwa ta kasa, Bubakar yacine Diallo, ya sanar manema labarai cewa, wannan sabuwar doka, ba karamin ci gaba ne ba, ta fannin karfafa demokaradiya cikin kasa.
Saidai ya ce akwai sharuda da gwamnati ta tanada, domin hakikance cewa wanda za su buda wannan kafofin sadarwa bazasu wuce gona da iri ba, a cikin shiryen shiryen su.
Haka zalika, dokar ta haramtawa jam´iyun siyasa ko kungiyoyin addini kafa gidajen rediyoyi.
Bugu da kari dokar bat a bada izinin mutum daya ya mallaki gidan redio ko talvejen fiye da daya ba.
Kuma bako, daga ketare ba zai ci moriyar wannan doka ba.
Jagoran yan adawa na Kasar Guinee, Alfa Konde yayi lale marhabin da matakin, duk da cewa bai taka karya bay a karya ga bukatoci masu yawa na al´ummar wanan kasa, ta fanning samun inganttacen cenji.
A yayin da ya ke bayana ra´ayin sa, shugaban mujjalar l´Independant ya shaidawa manema labarai cewa, wannan doka itace albishir mafi armashi da ya samu a shekara bana.
Shima Ba Mamadu, daya daga shuwagabanin jam´iyun adawa ya bayana mahimancin dokar ,ya kuma yi fatan gungun jam´iyun Frad, masu rike da ragama mulki, za su amince su sa baki a mahaurorin siyasa, da babu shaka za a shirya a sabin kafofin sadarwa.
Ya zuwa yanzu babu wani karin bayani daga gwamnati,a game da dalillan da su ka sa yanke wannan shawara, saidai masu kulla da harakokin siyasa a kasar, na nuni da cewa shugaba Lansana Kwante, ya yayi hakan ne, saboda matsin lamba, da ya ke samu daga ketare.