1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana hawa babura a yankin Diffa ta Nijar

Larwana Malam HamiFebruary 11, 2015

A wani mataki na inganta tsaro a yankin Jahar Diffa da ke gabashin Jamhuriyar Nijar inda sojoji ke dauki ba dadi da Boko Haram, gwamnati ta ayyana dokar haramta hawa babur a fadin yankin baki daya.

https://p.dw.com/p/1EZXF
Nigeria Angriff Miliz 19.03.2014
Hoto: Reuters

Dokar haramta hawa babur din dai ta zo ne a daidai lokacin da hare haren 'yan kungiyar ta Boko Haram suka fara tsamari a daf da karshen makon da ya gabata tare da kama hanyar mai da hanun agogo baya inda lamura suka kama hanyar sukurkucewa tare da saka mazauna birnin cikin zulumi na yin hijira.


Yankin na Diffa dai na daya daga cikin yankunan kasar da jama'a ke amfani da babura wajen gudanar da al'amurran su na yau da kullum.

A yanzu haka dai duk da irin matakan tsaron da hukumomi suka dauka a wani mataki na maido doka da oda jama'ar birnin na Diffa na ci gaba da kaura kuma suna kaura cewa ne cikin firgici kamar yadda wata mata ta sheda a lokacin da ta isa birnin Damagaram.

Bildergalerie Zinder Niger
Hoto: DW/ L.M. Hami

Kawo yanzu dai rohotanni daga jahar na cewar al'amurran tsaro da dama dama, kwanciyar hankali ta fara dawowa inda wasu majiyoyi da ba a tabbatar ba a hukumance ke cewar an sa hannu a kan wasu manya manyan mutane da ke da hanu a tada zaune tsayen da ake batu a kai.