1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar ta baci a Sudan ta Kudu

July 19, 2017

An kafa dokar ta baci a yankin arewacin Sudan ta Kudu sakamakon rikici kan filin gona da kiwo tsakanin 'yan kabilar Dinka.

https://p.dw.com/p/2gmCj
Äthiopien Addis Abeba Salva Kiir Mayardit und  Hailemariam Desalegn
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu ya kafa dokar ta baci cikin jihar arewaci da ya fito, a wani mataki na kawo karshen fada na cikin gida tsakanin 'yan kabilan shugaban.

Gwamnati ta ce an bai wa sojoji karfin ikon amfani da karfi wajen kawo karshen rikici a Jihar Gogrial. Haka za a yi aiki da dokar ta bacin a jihohi da ke makwabtaka. Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun hallaka sakamakaon tashin hankali tsakanin tsagerun bangarorin Apuk da Aguok wadanda duk 'yan kabilar Dinka ne.

An yi imanin wannan rikici na Sudan ta Kudu yana da nasaba kan filin kiwo da noma, yayin da ake samun karancin abinci cikin kasar.