1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar ta ɓace a birnin Quetta na Pakistan

August 27, 2006
https://p.dw.com/p/BulT

Hukumomin Pakistan sun kafa dokar ta ɓace a birnin Quetta, a sakamakon zanga -zangar da ta ɓarke , bayan mutuwar madugun yan awaren yankin Baluchistan, Nawab Akbar Khan Bugti, mai shekaru 79 a dunia.

Ranar jiya ne, a ka bayyana sanarwar mutuwar, a cikin wani hari da dakarun Pakistan su ka kai masa, a yankin Baluchistan.

Masu zanga zangar, sun ƙona kadarrori masu yawa, da su ka haɗa da, motoci da bankuna.

Rahotani daga jami´an tsaron Pakistan, sun ce a ƙalla, mutane 60 su ka rasa rayuka, daga ɓangarorin 2, a cikin arangamar da ta ta hadasa mutuwar madugun yan awaren.

Gwamnati ba ta bayyana lokacin ɗage dokar ta bacen da ta kafa ba,a yanki.

Saidai shugaban ƙasa Pervez Musharaf, ya gabatar da jawabi, inda ya alƙawarta saka magudan kuɗaɗe, domin kauyattata makomar al´ummomin wannan yanki.