Soma aiki da dokar tsaro a Hong Kong
July 1, 2020Talla
A ranar Talata 30 ga watan Yunin da ya gabata ne, dokar ta soma aiki gadan gadan biyo bayan majalisar dokokin China ta kada kuri'ar amincewa da ita, tare da bai wa kotun China damar zartar da hukunci ga wadanda aka kama da aikata mumunan laifi da ya saba dokar a yankin Hong Kong.
A yayin da take tsokaci game da sabuwar dokar a albarkacin ranar tunawa da sake komawar yankin a hannun kasar China, shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta yabawa sabuwar dokar da yanzu hakan ke ci gaba da haddasa cece-kuce, ta na mai cewa sabuwar dokar a matsayin wani sabon mataki da ka iya yin farraku da dagula al'amura na jagoranci na gari a yankin.