Afghanistan: Matakin 'yan Taliban na tada hankalin duniya
December 25, 2022A cikin wata sanarwar da ya babban jami'in harkokin wajenta Josep Borrell ya sakawa hannu, kungiyar tarayyar Turai ta yi kakkausar suka ga matakin 'yan taliban da ke jagorancin gwamnati a Afghanistan, tare da fatan gwamnatin za ta sake matsaya.
A yayin da babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ke bayyana kaduwa da sabuwar dokar, ita kuwa Majalisar Dinkin Duniya nuna matakin ta yi a matsayin na tauye 'yancin bani Adama.
Tuni har wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ke aikki a Afghanistan suka fara barazanar dakatar da aiki, ko kuwa fito da wasu sabbin dubaru na ci gaba da agazwa 'yan kasar da suka ce na cikin wani yanayi.
Wannan matakin na 'yan Taliban na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kungiyar Taliban ta sanar da haramtawa mata zuwa manyan makarantun illimi mai zurfi a kasar.