Dole ne a shigar da Iran da Syria don magance matsalolin Iraki
December 14, 2006Talla
Babban sakataren MDD mai barin gado Kofi Annan ya ce ba za´a iya warware rikicin Iraqi ba idan ba´a shigar da kasashen Iran da Syria wajen neman hanyoyin yin sulhu a cikin kasar ba. Mista Annan ya fadawa gidan radiyoon Faransa mai watsa shirye shirye zuwa ketare wato RFI cewa dole ne a shigar da kasashe makwabta. A lokaci daya Annan ya yi korafin cewa halin da ake ciki a Iraqi na tabarbarewa a kowace rana. Da farko Jordan da Iraqi sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda ta tanadi ba da hadin kai tsakanin kasashen makwabta a yakin da ta´addanci. Ita ma SGJ Angela Merkel ta jaddada shirin gwamnatin ta na shiga shawarwari da kasashen Syria da Iran. Ta ce ziyarar da ministan harkokin waje F-W Steinmeier ya kai birnin Damascus baya-bayan nan ba ta haifar da nasarar da aka yi fata ba cikin gajeren lokaci.