Dortmund na kan ganiyarta a Bundesliga
October 8, 2018Kungiyar Borussia Dortmund ta kare matsayinta na saman teburin Bundesliga inda ta doke takwararta ta Augsburg da ci hudu da uku, a wasanni mako na bakwai da suka gudana a karshen mako a sassa dabam-daban na Jamus. Godiya ta tabbata ga Paco Alcacer da Dortmund ta aro daga Barcelona wanda ya zura uku daga cikin kwallayen hudu. Borussia Dortmund na da maki 17 a yanzu, lamarin da da ya sa mai horaswarta Lucien Favre zama cochin da bai baras da wasa ko da guda ba tun bayan fara kakar wasanni.
Sai dai a daya hannun, Borussia Mönchengladbach ta bi Bayern har gida Munich ta kuma yi mata dukan kawo wuka ci uku da nema, lamarin da ya sa Mönchengldbach darewa matsayi na biyu da maki14, yayin da Bayern Munich ta koma matsayi na biyar. Wannan shi ne karo na hudu da kungiyar da ke rike da kambun zakara na Jamus ba ta tsinana komai a wasan da ta yi ba, kuma rabon da a ga irin wannan komabaya a tawagar tun shekara ta 2009.