1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Dortmund ta kori Nuri Sahin a matsayin mai horas da kungiyar

January 22, 2025

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta sallami mai horas da kungiyar Nuri Sahin bayan rashin nasara da kungiyar ta yi a fafatawarsu da Bologna a gasar Champions League inda aka tashi wasa 2-1.

https://p.dw.com/p/4pT8U
Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Dortmund Nuri Sahin
Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Dortmund Nuri Sahin Hoto: Michael Probst/AP/picture alliance

Dortmund ta yi rashin nasara a dukkannin wasannin da ta fafata guda hudu a wannan kaka tun daga farkon wannan shekara ta 2025. Kazalika kungiyar na fuskantar rashin tabbas a teburin wasannin Bundesliga na kasar Jamus inda take a matsayi na 10.

Karin bayani: Dortmund ta lallasa Freiburg da ci 4-0 

Babban daraktan kungiyar Lars Ricken ya shaida wa manema labarai cewa suna matukar bukatar Nuri Sahin, amma ba su da zabi illah yin bankwana da shi sakamakon rashin nasarar da kungiyar ke fuskanta, duk da cewa Sahin ya cancanci yabo.

Karin bayani: Fatan Jamusawa bayan nasarar Dortmund 

Hukumar gudanarwar kungiyar ta sanar da sunan Mike Tullberg a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar kwallon kafar ta Borussia Dortmund gabanin karawar da kungiyar za ta yi da Werder Bremen a mako mai zuwa.