1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiTurai

Draghi ya bukaci inganta masana'antun Turai

Suleiman Babayo AH
September 9, 2024

Tsohon firaministan Italiya ya bukaci kara zuba kari a bangaren masana'antun kasashen Turai

https://p.dw.com/p/4kQXV

Tsohon firamnistan kasar Italiya, Mario Draghi ya bukaci kungiyar kasashen tarayyar Turai ta bijiro da tsarin bisa manufa kan inganta masana'antun nahiyar domin zama masu gogayya da sauarn kasashen duniya.

Karin Bayani: An rusa majalisar dokokin Italiya

Draghi ya ce yanzu haka kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun kasance cikin yanayin da rashin samun ci-gaba da ake bukata saboda tsaffin matakan da ake aiki da su musamman idan aka kwatanta da kasashen Amurka da Chaina.

Shi dai Mario Draghi tsohon firaministan kasar ta Italiya ya taba jagorancin babban bankin kasashen Turai, kuma yanzu ya nemi ganin kara zuba jari a bangaren inganta masana'antu tsakanin kasashen Turai.