Dubbai na cikin mawuyacin hali a yankin Afar na Habasha
February 8, 2022Talla
Gwamnatin yankin Afar da ke Habasha, ta ce sama da mutum dubu 300 ne suka rasa muhallansu daga watan Disambar bara zuwa yanzu, tana mai dora laifi a kan mayakan yankin Tigray.
Baya ga wannan zargi na daidaita mutane a yankin, hukumomin na Afar sun ce mayakan na Tigray sun kakkashe mutane tare da sace dukiyoyi masu yawa a yankin.
Ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici a yankin na Afar, ya hana ta damar kai kayayyakin jin kai ga dubban mabukata da ke a a yankuna masu makwabtaka da Tigray da matsalar fari ta shafa.
Cikin watan Nuwambar 2020 ne dai fada ya barke tsakanin gwmanatin Habasha da kawayenta ciki har da wadanda ke a yankin na Afar, da kuma mayaka masu fafutikar kare al'umar Tigray.