1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma na guje wa hare-hare a Siriya

Yusuf BalaOctober 20, 2015

Mutanen na cikin yanayi na mutukar bukata musamman ta abinci da makwanci a Syriya a daidai lokacin da ake shirin tunkarar sanyin hunturu.

https://p.dw.com/p/1GrAP
Europa Kos Flüchtlinge Migranten Versorgung
'Yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa/S. Palacios

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sabbin hare-hare da aka kaddamar a Siriya bisa jagorancin Rasha sun yi sanadin kisan mutane 370 mafi akasarinsu fararen hula. An dai samu mutane 35,000 da suka rabu da muhallansu musamman a Kudu maso Yammacin birnin Aleppo cikin 'yan kwanakin nan a cewar Vanessa Huguenin da ke magana da yawun ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke lura da ayyukan jinkai OCHA.

Ta ce mutanen da ke gudun hijira na zaune ne da 'yan uwa da abokan arziki a wurare da hukuma ba ta san da su ba a yammacin lardin, ta kara da cewa mutanen na cikin yanayi na mutukar bukata musamman ta abinci da makwanci ga shi kuma ana tunkarar hunturun sanyi.

Tun dai daga watan Maris na shekarar 2011 , rikicin na Siriya ya sanya mutane 250,000 sun rasu sannan miliyoyi sun kauracewa muhallansu.