1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dubban bakin hauren na nuna bukatar komawa gida

June 27, 2024

Ana ci gaba da samun daruruwan bakin haure masu neman shiga Turai da ke komawa kasashensu bisa radin kansu. Hakan na faruwa ne yayin da suka makale a kasar Tunisiya da ke arewcin Afirka.

https://p.dw.com/p/4hbhK

Ana samun karin bakin hauren da ke a Tunisiya a halin yanzu wadanda ke zabar a maida su kasashensu na asali, a cewar hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya wato IOM.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai da bakin hauren ke neman shiga ala kulli halin, ke matsawa a kan dakile shigowar bakin.

Daga ranar daya ga watan Janairun bana zuwa 25 ga wannan wata na Yuni dai, hukumar IOM din ta ce tsara mayar da bakin kasashensu bisa radin kansu da suka kai yawan mutum dubu uku da 500.

Shirin wanda ke daukar nauyin biyan kudin jirgin, ya ga karuwar kashi 200 na wadanda ke son komawar a bana, bayan aniyarsu tun farko ta shiga Turai ta barauniyar hanya, idan aka kwatanta da yadda yake a bara.