Dubban Falasdinawa sun rasa rayukansu
October 28, 2023A cewar sanarwar da hukumomin Gaza, sama da dubu 3,500 kananan yara ne.
A daren jiya ne Isra'ila ta kaddamar da wani sabon hari ta sama da kasa a Gaza, inda rahotanni suka ce sama da jiragen yaki 100 ne suka yi luguden wuta a wani yunkuri na kakkabe mayakan Hamas. An dai katse hanyoyin sadarwa a illahirin yankin da ma wutar lantarki.
Kakain rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari, ya ce kutsen ta kasa, munafarsa shi ne kame wasu yankuna a arewacin Zirin da kuma ragargaza wasu runbunan makamai da tungogin mayakan Hamas.
Karin bayani: Sojojin Isra'ila sun kutsa Zirin Gaza ta kasa
Dubban gidaje ne wannan sabon harin ya lalata inji hukumomin Hamas.
Harin na zama mafi muni da ba a ga irinsa ba kwanaki 21 tun bayan barkewarsa.
Shugaba Recep Tayyip Erdogang na Turkiyya ya kira wannan sabon harin na Isra'ila a Gaza da na rashin hankali da imani, ya kuma nemi 'yan kasar da su fito tattakin nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu.