1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban fararen hula na tserewa Gouta

Abdul-raheem Hassan
March 15, 2018

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Syrian Observatory for Human Right, ta ce akalla fararen hula dubu 7,000 dauke kaya da kananan yara da mata ke kauracewa garin Hammouriyeh sakamakon fargabar barin wuta

https://p.dw.com/p/2uNjk
Irak Bagdad Flüchtlinge aus Ramadi
Hoto: Reuters/Stringer

A yanzu dai sojojin gwamnatin Siriya na ci gaba da mamaye yankunan da 'yan tawayen ke iko da su, inda rahotanni ke cewa dakarun sun yi nasarar kwace kashi 60 na yankunan 'yan tawayen tun bayan kaddamar da zafafa hare-hare wata guda da ta gabata.

A yanzu dai Siriya ta shiga shekara na Takwas da fara fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye, abinda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula akalla dubu 3,000 yayin wasu dubbai ke gudun hijira a sauran kasashen duniya.