1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban likitoci na cikin hadari a Spain

March 30, 2020

Kimanin likitoci da sauran jami'an lafiya dubu 12 da 300 ne suka kamu da cutar coronavirus yayin aiki a Spain, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta sanar a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/3aCJ2
Spanien Ebola Krankenhauspersonal 7. Oktober
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Paul White

Wannan adadi dai a cewar hukumomin na spain, ya kai kamar kashi 14% na yawan wadanda cutar ta kama ke nan yanzu a Spain, inda ake da mutum dubu 85 da 195.

Akwai kuma akalla mutum dubu 7 da 340 da annobar ta salwantar yanzu a kasar, inda cikin sa'o'i 24 da suka gabata ta kashe 812.

An dai yi tsit na minti guda a fadin kasar don nuna alhinin mutuwar da cutar ta haddasa kuma take kan haddasawa cikin dan kankanin lokaci da ta fara.

A yanzu dai kasar ta Spain ta zamo ta uku da ta sha gaban China da yawan wadanda ta yi tsanani a cikinsu, bayan kasashen Amirka da kuma Italiya.