Dubban mutane na komawa Arewacin Gaza
Duk da gargadin da sojojin Isra'ila suka yi, dubban Falasdinawa da aka yi wa kawanya sun yi tattaki daga Kudu domin komawa arewacin Zirin Gaza.
Hijira daga Kudu zuwa Arewa
Dubban Falasdinawa sun yi tattaki ta gabar teku daga kudu zuwa arewacin Zirin Gaza. Sun dauki wannan mataki duk da cewa sojojin Isra'ila sun yi gargadin cewa har yanzu yankin Arewa na zama yankin da ake gwabza fada. Sai dai fatan janyewar sojoji a Arewa da fargabar kai farmakin soja a kudancin kasar ya sa su komawa gidajensu, duk da cewa an lalata su.
Yankunan da aka lalata
Yankuna da dama na Zirin Gaza ne sojojin Isra'ila suka lalata don mayar da martani ga mummunan harin ta'addancin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Kusan rabin al'ummar yankin miliyan 2.3 sun guje wa fadan zuwa kudancin zirin. Amma da yawa sun fara komawa Khan Yunis, inda gine-gine da yawa suka lalace.
Takardun gargadi
Sojojin Isra'ila sun rarraba takardu domin yin gargadi ga mutane cikin harshen Larabci game da "yanki mai hatsari na yaki" a arewacin Gaza. Wasu iyalai da suka koma Beit Hanoun da Jabalia a makonnin da suka gabata, bayan janyewar sojojin Isra'ila, sun sake barin wurin saboda fargabar barkewar wani sabon fada.
"Muna son gidajenmu"
Tun tsawon watanni, wadanda suka rasa matsugunansu suna zama a karkashin tantuna a sansanoni da makarantu da kuma gidajen dangi a kudancin Zirin Gaza. "Muna son gidajenmu, muna son rayukanmu, muna so mu koma, ko ba a tsagaita wuta ba," in ji wata mace da ake kira Ummu Nidhal Khatab a kan hanyarta ta komawa Arewacin Zirin Gaza.
Wahala, 'yunwa da rashin isasshen taimako
Halin da ake ciki na jin kai a Zirin Gaza yana da muni. Bayan watanni shida na yaki, kusan mutane miliyan daya na fama da 'yunwa. Akwai fatan cewa kayan agajin da ake harbawa ta sama za su iya rage wahalhalun da ke addabar arewacin zirin, sannan Isra'ila ta bude sabbin hanyoyin kai kayan agaji. Sai dai a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yawancin kayan agajin ba sa kaiwa ga mutanen da ke bukata.
Harbe-harbe a wani shingen bincike
Tafiya zuwa arewacin Zirin Gaza na da hadari. Shaidun gani da ido sun sanar da cewa, an yi harbe-harbe a wani shingen bincike da sojojin Isra'ila ke da iko a hanyar shiga yankunan arewaci. Asibitin Awda da ke tsakiyar Zirin Gaza ya ba da rahoton mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu 54. Sojojin Isra'ila ba su ce komai kan wannan batu ba.
Mage a cikin jaka
Wani yaro ya kula da kyanwarsa a kan hanya mai hadari ta zuwa Arewacin Gaza. Yakin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula Falasdinawa sama da 34,000, kuma akalla 13,000 daga cikinsu yara ne. Kimanin mutane miliyan 1.8 sun rasa matsugunansu. Gagarumar matsalar jin kai na shirin kunno kai, a daidai lokacin da wasu sassan yankin ke fuskantar yunwa. Ba a kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta ba.