Dubban mutane na tserewa daga yankin 'yan tawaye a Aleppo
December 1, 2016Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kusan dubu 30 ne suka tsere daga wani yankin da ke karkashin ikon 'yan tawaye a birnin Aleppo na kasar Siriya, lamarin da ya sanya adadin mutanen da suka rasa gidajensu a yammacin birnin ya zarta dubu 400, inda suke fuskantar tsananin sanyin hunturu da ke tafe. A lokacin da yake magana da manema labarai, mai ba wa wakili musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya shawara, Jan Egeland ya ce Majalisar Dinkin Duniya na aiki domin tatara wadannan mutane.
"A cikin kwana guda mun yi rajistar mutane dubu 18 a yankunan da ke karkashin ikon dakarun gwamnati. Dukkansu dai sun fito ne daga gabacin Aleppo, yawansu na iya karuwa. Mun kuma yi rajistar wasu 8,500 a yankin Kurdawa na Cheikh Masoud."
Jami'in ya zargi Rasha da gwamnatin Siriya da kin tsagaita wuta a ruwan bama-baman da suke yi don bada damar kai magunguna da abinci a gabacin Aleppo.