Dubban mutane sun halarci gangamin nasara a Zirin Gaza
August 27, 2014Dubun dubatan mutane ne suka halarci wani babban gangami a Zirin Gaza don murnar nasarar da kungiyar Hamas ke ikirarin ta samu a rikicin da ta yi da Isra'ila. A jawabin da ya yi wa taron gangamin shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya ce kungiyarsa ce ta yi magana ta karshe yna mai cewa: "a lokacin gumurzun na tsawon kwanaki 51, mayakan Qassam da baradan fafatuka suka yi galaba. Sun fara yakin da kai hari a kan Haifa sannan suka kammala shi da wani harin a kan Haifa."
A kuma halin da ake ciki manyan motoci dauke da kayan agaji na Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya sun shiga Zirin Gaza daga Masar da kuma Isra'ila a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas tana aiki. Wannan shi ne karon farko tun shekarar 2007 da wani ayarin motocin agaji na hukumar ya samu nasarar tsallakawa cikin Gaza daga Masar.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahmane Hassane