Dubban 'yan gudun hijira sun mutu a teku
September 29, 2023Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 2,500 ne suka salawanta a tekun Bahar Rum kadai a wannan shekarar, a yayin da suke kokarin shiga kasashen Turai ba bisa ka'ida ba.
Hukumar kula da agaji ta majalisar duniyar UNHCR, wadda ta nuna damuwa, ta kuma ce a bana bakin hauren da suka mutun sukaru sama da abin da aka gani a daidai wannan lokaci a bara. A baran dai mutum dubu da 680 ne aka yi kiyasin suka mutu a tekun.
Alkaluma dai sun nunar da cewa kimanin bakin haure dubu 186 ne suka shigo nahiyar Turai ta tekun a tsakanin watan Janairu zuwa 24 ga wannan wata na Satumba da muke ciki.
Daga cikin su akwai dubu 130 wadanda ke a Italiya a yanzu, saura dubu 500 kuma na kasashen Girka da Spain da Cyprus gami da tsibirin Malta.
Akasarin bakin na haure dai sun fito daga kasashen Afirka bakar fata.