1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Sudan na neman mafaka a Chadi

Binta Aliyu Zurmi
May 23, 2023

Mutum dubu 60 zuwa dubu 90 ne hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNCHR ta ce sun gudu daga Sudan ya zuwa kasar Chadi tun bayan da rikici ya barke a kasar a tsakiyar watan Afirilu.

https://p.dw.com/p/4Rh14
Sudan Flüchtlingswelle
Hoto: Gueipeur Denis Sassou/AFP

Kazalika hukumar ta UNCHR ta ce sama da mutane dubu 250 ne suka fice daga kasar da ke fama da rikicin shugabanci, wanda sama da kaso 90 cikin 100 na wadannan mutanen mata ne da kananan yara, kuma ana sa ran adadin ka iya karuwa.

A wata ziyarar gani da ido da wani babban jami'in hukumar ta 'yan gudun hijira Raouf Mazou ya kai kasar Chadi, ya ce akwai bukatar samar wa 'yan gudun hijirar da ke isa Chadi matsugunai a yayin da damina ke shirin kankama.

A jiya Litinin ce dai aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, sai dai babu tabbacin ko bangarorin biyu za su mutunta wannan yarjejeniyar kamar yadda aka gani a baya, wasu majiyoyi sun tabbatar da jiwo amon harbe-harbe a sararin samaniyar birnin Karthoum.