1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dumamar yanayi na kara matsalar yunwa a Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
October 15, 2019

Jamhuriyar Nijar na ci gaba da kasancewa daya daga cikin kasashen Afirka da 'yunwa ke addaba duk da kokarin hukumomin kasar, a cewar rahoton shekara-shekara da kungiyar Welhungerhilfe ta kasar Jamus ta fitar.

https://p.dw.com/p/3RLQA
Niger Dürre Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kungiyar Welthungerhilfe ta nunar da cewar Jamhuriyar Nijar ta kasance a sahu na 16 daga cikin kasashe 117 na duniya da ke fama da yunwa. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da matsalar dumamar yanayi da ke haddasa karancin abinci a kasar ta Nijar.  Amma kuma wannan matsalar ta ja baya idan aka kwatanta da shekaru taran da suka gabata, sakamakon kokarin da gwamnati ke yi wajen wadata kasar da abinci. Sai dai Kungiyar ta Jamus ta ce dalilai uku ne suka jefa kasar ta yammacin Afirka ciki da rikice-rikice da ake fama da su a wasu sassa na kasar ciki har da ta'addaci a yankin Diffa, da matsalar sauyin yanayi da ke haddasa ambaliya ruwa da fari, lamarin da haifar da asarar amfanin gonaki a shekaru 10 na baya-bayannan. Sannan kuma baya ga karuwar al'umma cikin hanzari da ake fuskanta a kasar, talauci na ta'azzara 'yunwa a kasar. Ko da Francis Djomeda, shugaban reshen Welthungerhilfe a Nijar sai da ya dora wannan laifi kan dumamar yanayi.
 
"Ba wai muna nufin cewar dumamar yanayi ne ya haddasa yunwa a Nijar ba, amma tana taimakawa wajen ta'azarar matsalar. Ga misali idan ana fara damina kafin lokacin da aka saba, kuma ruwan sama ya katse da wuri, yayin da kaka ke dadewa fiye da shekarun baya, lamarin da ke mummunan tasiri ga rayuwar yau da kullum, ma'ana mutane ba sa samun amfani gona."

Afrika Hungerkatastrophe Archivbild 2005
Hoto: picture-alliance/dpa

Yara da shekarunsu ba su zarta biyar da haihuwa sun fi fama da ja'ibar ta 'yunwa a Jamhuriyar Nijar sakamakon karancin abinci maras gina jiki musamman ma a yankin Maradi da Agadez. Yayin da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasuwannin kasar ke sa wasu 'yan kasa ba tare da sa abu a bakin salati ba. Duk da cewa Jamhuriyar ta Nijar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Maputo da ke tilasta wa gwamnatoci Afirka kawar da 'yunwa kwata-kwata daga kasashensu nan zuwa shekara ta 2030, amma ana ganin cewar da kamar wuya Nijar ta cika wannan sharadi, alhali 'yunwa ta ragu da kashi 30% a kasar. Francis Djomeda na kungiyar Welthungerhilfe a Nijar ya ce suna iya kokarinsu don rage kaifin 'yunwa a kasar.

Afrika Dürre
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo


"Muna kawo dauki cikin gaggawa ta hanyar raba abinci kama daga gero zuwa dawa da mai da sabulu da ruwa. Amma kuma muna taimaka wa al'umma tashi tsaye don taimaka wa kansu da kansu. Muna taimaka musu da taki na zamani, wadanda ba sa bukatar ruwan da yawa, amma ake girban amfaninsu cikin gaggawa, wadanda kuma kwari da sauran cututtuka ba za su lalata ba."

Ko da shi ke wasu kasashe da ke makwabta da Nijar na fama da 'yunwa irin su Mali da Burkina Faso, amma matsalar ba ta kai girman ta Jamhuriyar ta Nijar ba. Sai dai kungiyar WeltHungerhilfe ta ce akwai bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnatin Nijar da manoma da sauran masu ruwa da tsaki wajen gano bakin zaren warware matsalar ta 'yunwa a jamhuryair Nijar.