Fitar da hayaki mai guba na karuwa a duniya
November 21, 2023Talla
Majalisar wacce ta gabatar da rahotonta na shekara-shekara a kan dumamar yanayin a birnin Nairobi na Kenya ta ce duniya na fuskantar babban hadari.Ta kuma ce tana da fargaba game da fitar da hayaki mai guban wanda kan iya wuce matakin da aka cimma a yarjejeniyar yanayi Paris a shekarara ta 2015. Yarjejeniyar ta tanadi rage fitar da hayaki mai guba da ke gurbata muhali da akalla kashi 28 zuwa kashi 42 cikin dari a cikin shekaru goma masu zuwa. MDD ta bayyana wannan rahoton ne kwanaki kadan gabanin taron sauyin yanayi na duniya COP28, wanda za a yi a ranar 30 ga Nuwamba a Dubai.