Kasashe na tayin kai wa Turkiyya agaji
February 6, 2023Talla
A jawabin da ya yi da aka yada ta akwatunan talabijin, Erdogan ya ce adadin mutanen da suka rasu sun kai mutum 912 yayin da wasu 5,400 kuma suka jikkata. An kuma ceto mutane 2,470 daga baraguzan gine-gine.
Gidaje kimanin 3,000 suka ruguje a girgizar kasar. Baki daya mutanen da suka rasu a girgizar kasar a Turkiyya da Syria sun haura mutum 1, 400
Sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce mambobin kawancen kungiyar suna gangami domin taimaka wa Turkiyya tunkarar kalubalen iftila'in.
Rasha ta ce za ta tura ma'aikatan ceto zuwa Turkiyya domin taimaka wa Turkiyyar da makwabciyarta kasar Syria.