SiyasaLebanon
Duniya na maraba da sabon shugaban Lebanon
January 9, 2025Talla
Sabon shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun ya shaida wa 'yan majalisar dokoki cewa kasar ta shiga sabon babi a yayin da ya gabatar da jawabinsa na farko bayan zabarsa.
Jim kadan bayan rantsar da shi, shugaban kasar ya bukaci 'yan majalisar su fara tattaunawa domin nada sabon Firaminista.
Ministan harkokin wajen Israila Gideon Saar ya taya Aoun murna kan zabensa, yace yana fata matakin zai kai ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Iran ita ma ta taya Aoun murna a wata sanarwa da ofishin jakadancin Iran din a Lebanon ya wallafa a shifin X inda ya baiyana fatan za su aiki tare ta fannoni da dama da za su amfani al'umomin kasashen biyu.