1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNa duniya

Coronavirus na kara yaduwa a duniya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana samun karuwar rahoton wadanda suka kamu da cutar coronavirus a duniya, inda ta ce an samu sama da mutane dubu 230 da suka kamu da ita cikin sa'o'i 24 kacal.

https://p.dw.com/p/3fCXs
Brasilien | Coronavirus-Ausbruch in Sao Paulo
Karuwar masu kamauwa da coronavirus a duniyaHoto: Reuters/M. Moraes

Rahoton na Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ya nunar da cewa, kasashen da aka fi samun karuwar wadanda suka kamun a rana guda sun hadar da Amirka da Brazil da Indiya da kuma Afirka ta Kudu. Rahoton sababbin kamuwa da cutar na baya-bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO ta fitar dai, na nuni da cewa mutane sama da dubu 228 ne ke kamuwa a kowacce rana, yayin da adadin wadanda cutar ke yin ajalinsu a kullum ya kasance kimanin 5,000.

A wani kiyasi na kamfanin dillancin labarai na Reuters, kawo yanzu adadin wadanda suka kamu da annobar cutar ta coronavirus a duniya ya tasamma miliyan 13, abin da ke nuni da cewa cutar da aka tabbatar ta halaka sama da mutane dubu 565 a duniya cikin watanni bakwai, na ci gaba da yaduwa.