China ta sasauta dokokin corona
December 29, 2022Kasar Amirka ta kasance kasa ta baya-bayan nan da ta dauki matakan yaki da corona ga matafiya 'yan China da ke shiga kasarta. Tuni dai kasar Amirka ta ce daga ranar biyar ga watan Janairun badi, sai an yi wa 'yan Chaina da ke shiga kasar gwajin cutar Corona na wajibi. Hakan dai ya biyo bayan sassauta wasu dokoki ciki har da bude iyakoki da Chaina ta yi duk da cutar na cigaba da yaduwa a kasar. Ko a ranar Litinin din da ta gabata ma gwamnatin Beijing ta sanar da cewa za ta janye dokar wajabta killace kai bayan isa kasar. Ana dai ganin Chainar na sassauta dokokin dakile yaduwar cutar ce sakamakon bore da 'yan kasar suka yi ta yi kan a sassauta dokokin.Tun da fari kasashen Japan da Indiya da Italiya da Taiwan da kuma Japan sun dauki irin matakin da Amirka ta dauka. Sai dai kuma wasu kasashen sun ce ba za su dauki matakan sanya sabbin takunkumai na yaki da cutar. Christofer Burger da ke zama kakakin gwamnatin Jamus ya ce Jamus ta fara nazarin kan matakan da za ta dauka.Ya ce " Duk da cewa takumkuman da ake sanya wa matafiya da suka fito daga Chaina saboda yaki da annobar corona, a don haka muka fara yin nazari kafin daukar wasu matakai, amma kafin nan muna gwamnatin tarayya na bin abubuwan da ke gudana sau da kafa."
Kasashen duniya ba su yarda da matakin da Chia ba ta dauka
Firaministan Australiya Anthony Albanese. Ya ce: " Alal hakika za mu ci gaba da lura da yadda lamura ke wakana a Chaina da ma wasu sassan duniya kamar yadda muke yi. Za mu dauki shawarwarin da suka dace daga masanin kiwon lafiya da kuma kwararru. Kawo yanzu ba za mu sauya tsare-tsaren tafiye-tafiye amma dai muna ci gaba da sanya ido. Babban abun da muka saka a gaba shi ne kula da lafiyar 'yan Australiya. Chaina dai ta yi amnar cewa akwai bukatar kasashe su dauki matakai ne a kimiyyance kana kada ya shafi tsarin tafiye-tafiye a cewar ministan harkokin wajen Chaina Wang Wenbing: Ya ce " A halin yanzu, akwai bukatar a yaki cutar ne ta hanyar kimiyya tare da yin aiki tare wajen tabbatar da tsaron lafiyar matafiya daga kasashe dabam-dabam. Mun lura da cewa wasu kasashen duniya na amfani na nuna kyawawan dabi'u, muna fatan samun cigaba kyautata mu'amulla tsakanin 'yan Chaina da kuma kasashen ketare." Ana dai zargin Chaina da yin rufa-rufa kan alkalumma masu kamuwa ko ma mutuwa sanadiyar cutar, inda alkalumma suka nuna cewa cikin kwanaki bakwai da suka gabata mutum 1 ne kacal ya mutu sanadiyar cutar a kasar.