Kasashen duniya sun ji takaicin harin Hamas a Isra'ila
October 9, 2023To kusan dai ko wacce kasa ta yi Allah wadai da tashin hankali, inda misali kasar Turkiya shugabanta Raccip Tayyip Erdowan ya yi tir da hare-haren, kuma ya sanar da cewa kasarsa a shirye take don shiga tsakani a samar da masalaha tsakanin Isra'ila da Falasdinu. Ita kuwa Firimiyar Italiya, ta kira takwráranta na Isra'ila Benjamin Netenhayu don jajanta masa. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Schulz wanda Jamusawa 'yan kasarsa ke cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ya ce Jamus ba wai tana tare da Isra'ila kawai ba, amma Berlin za ta yi duk iya kokarinta don ganin ta'addanci bai yin asara ba. Scholz ya ce gaba da cewa: "Muna yin Allah wadai da babbar murya bisa matakin na Hamas. Musamman, muna yin duk abin da za mu iya don ganin cewa wannan harin bai rikide zuwa wani tashin hankaliba wanda ba za a iya shafuwar daukacin yankin. Kuma muna gargadin kowa da kowa game da rura wutar da kuma ci gaba da ta'addanci a cikin wannan yanayi".
Rasha ta yi kira da a samar da 'yancin gashin kai na Falasdinu
A martaninsa ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta shi ne kawai zai iya kawo karshen wannan tashin hankalin, inda Lavorov ya ce yaki da ta'addanci kadai ba zai iya magance rikicin Isra'ila da Falasdinu ba."Zabi daya ne kawai na warware rikicin Falastinawa Wato shi ne samar da kasashe biyu a matsayin makwabta da ke wanzuwa Isra'ila da Falasdinu. Wannan shi ne daidai. Wannan shi ne matsayinmu na bai daya, kuma wannan shi ne kawai shirin da zai iya kasancewa a kan teburin da zai iya zama don yin shawarwari kai tsaye tsakanin kasahen biyu.
Kokarin tsagaita wuta a yakin da ke yin barazana ga bazuwa a yankinSakatare janar na kungiyar Larabawa Ahmed Aboul Gheit,wanda ke ziyara a Rasha,ya bayyanan cewa da shi da ministan harkokin wajen Rasha sun amince da a kawo karshen wannan tashin hankalin nan take, kuma cewarsa, wannan matsalar hare-hare ba ta kare ba muddin baa kai ga magance matsalar Farasdinawa ba, inda ya ce."Na yarda cewa dukkanmu ba mu amince da duk wani harin da aka kai wa farar hula ba, amma dukkan fararen hula, ba farar hular wata kasa ko wani bangare ba". Daga Kasar Japan ma hukumomi sun yi matukar Allah wadai da harin da Hamas ta kai, a cewar ministan harkokin waje, Yoko Kamikawa, kana ya kara da cewa haka zalika Japan ta damu matuka bisa yawan mutanen da ke mutawa cikin Gaza biyo martanin da Isra'ila ke yi. Kawo yanzu dai ba a kai ga samun tsagaita wuta ba tsakanin bangarorin biyu, abin da ya nuna cewa da jan aiki izuwa sa'o'i ko kuma kwanaki da ke tafe.