Duniya tayi marhabin da hukunci kan Charles Taylor
April 27, 2012Ranar Alhamis, kotun shari'ar masu aikata manyan laifukan yaki a birnin Hague ya sanar da cewar ya sami tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor da laifin yaki da kisan jama'a a kasar sa ta Liberiya da Saliyo. Jaridu da dama sun maida hankalin su kan wannan hukunci da kuma abin da hakan ke nufi gareshi da wadanda ya aikata laifin a kansu.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace Charles Taylor shine tsohon shugaban wata kasa na farko da aka gabatar dashi gaban kotun kasa da kasa tun shekara ta 1946, da aka same shi da laifi saboda yaki rashin imani a lokacin yaki. Ko da shike sai a watan gobe ne kotun a Hague zai sanar da hukuncin da za'a zartas a kan tsohon shugaban, amma bisa dukkan alamu, hukuncin daurin rai da rai ne zai hau kansa. Musamman kotun ya maida hankalin sa ne ga aiyukan rashin imani da zub da jini da aka zargi Taylor da aikatawa a lokacin yakin basasa a Saliyo a tsakanin shekarata 1991 zuwa 2002, inda akalla mutane 120.000 suka mutu. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace daya daga cikin manyan laifukan Taylor, shine daurawa yan tawayen Saliyo na kungiyar RUF damarar makamai, inda a madadin haka, yan tawayen suka yi masa sakaiya da diamond da suka rika hakowa ta hanyoyi na haramun.
A sharhin ta a wannan mako, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba kasar Guinea Bissau, inda sojoji suka aiwatar da juyin mulki makonni biyu da suka wuce. Jaridar tayi nuni da yadda sojojin da suka kawar da gwamnati da kuma jam'iyu na adawa suka gaggauta cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin wucin gadi da zata jagoranci kasar tsawon shekaru biyu kafin zabe na gaba. Wannan mataki an dauke shine domin kaucewa shisshigin kungiyar ECOWAS ta kasashen Afrika ta yamma da kungiyar hade kan Afirka, wadanda tun bayan juyin mulkin suke barazanar tura sojojin hadin gwiwa domin sake maido da democradiya a kasar da ta taba zama karkashin mulkin mallakar Portugal. Karkashin tsarin da aka yi, za'a rushe majalisar dokoki, za'a kuma sauke Pirayim minista Gomes Junior da shugaban kasa, yayin da masu juyin mulkin suka yi alkawarin sannu a hankali zasu mika mulki gaba daya zuwa ga gwmanatin ta wucin gadi da za'a nada.
Halin da ake ciki na zaman doya da manuja tsakanin Sudan ta kudu da Sudan ta arewa, ya dauki hankalin jaridu a wannan mako a nan Jamus, inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace kasashen biyu suna neman shiga yakin da a zarihi babu mai iya tafiyar dashi, saboda rikicin ya sanya dukan su suna asarar rijiyoyin man da suke mallaka, wadanda, musmaman a Sudan ta kudu, sune tushen kudaden da take samu domin tafiyar da aiyukan ta na yau da kullum. Ya zuwa yanzu a dauki ba dadi tsakanin kasahen na Sudan ta kudu da Sudan ta arewa, an yi kiyasin cewar sojojin Sudan ta kudu fiye da 1200 ne suka mutu, yayin da Sudan ta arewa ta rasa mafi yawan arzikin da take samu daga man fetur a iyakokin da ake rikici kansu. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace lokacin da Sudan ta kudu ta baiwa kanta mulkin kai a bara, duniya gaba daya ta nuna farin ciki, inda aka manta da gaskiyar cewar bayan ballewar yankin na kudu daga arewa, kungiyar SPLA da tayi shekara da shekaru tana gwagwarmayar neman yanci, bata da wani tsayaiyen shiri ko tsari na ci gaban kasa. An kasa daidaita tsayaiyyun ikoki tsakanin yankunan na arewa da kudu, an kuma kasa tantance yadda za'a yi rabon arzikin man fetur dake tsakanin iyakokin nasu. Wadanda suka goyi bayan gaggauta baiwa yankin na Sudan ta kudu mulkin kansa, tilas yanzu su amsa laifin abubuwan dake faruwa a kasar ta Sudan, inji jaridar.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Abdullahi Tanko Bala