DW Rediyo da DW TV Zaure ɗaya suke watsa shirye-shiryensu?
July 8, 2012Tashar DW ta fara watsa shirye-shiryenta ta rediyo a shekarar 1953, to amma bata fara gabatar da shirye-shiryen talabijin ba sai a shekarar 1992. Kuma tun daga wannan lokaci, shirye-shiryen ke zuwa daga birnin Berlin.
A shekarar 1953 lokacin da aka fara shirye-shiryen Rediyo, suna zuwa ne daga birnin Kolon. Idan masu sauraro basu manta ba a da can bayan an kammala shiriye-shirye, akan ce "daga sashen Hausa da ke birnin Kolon" .
To amma an raba waɗannan fannoni na shirye-shirye guda biyu. A yayinda ake watsa shirye-shiryen rediyo daga Kolon, shi talabijin, tun tushen sa a Berlin ya ke kuma har zuwa yanzu. Ko da shi ke Deutsche welle ta taso baki ɗaya daga Kolon din ta dawo ban wanda ya ke ba nisa ne na abun kirki ba to amma shirye-shiryen talabijin sun cigaba da kasancewa a Berlin kamar yadda suke tun a farko.
Yawan Sassan da tashar Talabijin ta ƙunsa
A watan Afrilun shekarar 1992 lokacin da aka fara shirye-shiryen an fara ne da harsuna guda biyu wato da Ingilishi da kuma Jamusanci. Bayan shekara guda sai aka ƙara da harshen Spanianci. Daga wannan lokacin zuwa yanzu, an ƙara harsuna da dama waɗanda a cikin su akwai Dari da Pashtu, waɗanda harsuna ne na ƙasar Afghanistan saboda halin da ake ciki na yaƙi. Akwai kuma harshen Larabci saboda yankunan Masar, Arewacin Afirka da Duniyar Larabawa. Harsunan da Talabijin ke watsa shirye-shiryensu basu kai yawan na Rediyo ba. Harsunan kimanin shidda ne a yayin da Rediyo ke da 30
Alaƙar Tashoshin biyu da tsarin shugabanci
Deutsche Welle gaba ɗaya ko Talabijin ko Rediyo shugabansu ɗaya ne wanda shien Darekta Janar, to amma a ƙasarsa akwai Darektoci daban-daban, misali akwai Darektan da ke kula da Talabijin akwai kuma na Rediyo amma dukkansu na ƙarƙashin jagorancin Darekta Janar ne wanda a yanzu haka shine Erik Bettermann. Yana da ofishinsa a Berlin da kuma nan Bonn, to amma Darektocin na taimakawa sosai saboda ba zai iya kasancewa a duk wuraren biyu a lokaci guda ba.
Tsarin aiki da cuɗanya tsakanin ma'aikata
Bisa manufa ma'aikacin Talabijin da na Rediyo a nan Deutsche Welle duk abu guda ne, ƙarƙashin tsari guda suke, ƙarƙashin dokoki ɗaya suke ƙarƙashin hukuma ɗaya suke. Yanayin albashinsu ɗaya ne. To amma idana aka cire duk waɗannan abubuwa, akwai horo, wanda yake horon da ake baiwa ma'aikacin Rediyo ba ɗaya ne da wanda ake baiwa ma'aikacin Talibijin ba. Idan har ya kasance ma'aikacin Talabijin ya iya na Rediyo babu wani banbanci sosai.
To sai dai akan sami wannan canji a tsakanin ma'aikatan da ke kula da al'amuran yau da kullun, wato ka bar ofishin na Bonn ka je Berlin amma tsari ɗaya ne in banda banbancin gari saboda suk dodo ɗaya akewa tsafi.
Mawallafa: Umaru Aliyu/Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal