1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW ta karrama gwarzon dan jarida na bana

Suleiman Babayo M. Ahiwa
June 20, 2023

Taron shekara-shekara na Global Media Forum da tashar DW ke daukar nauyi ya fara gudana, inda 'yan jarida ke muhawa a kan kokarin magance rarrabuwar kanu da ke mai muni.

https://p.dw.com/p/4SmZ6
Gwarzon dan jarida 0scar Martinez
Hoto: Bjorn Kietzmann/DW

Taron 'yan jaridu daga sassan duniya ke halarta a bana an yi masa taken shawo kan matsalar rarrabuwa da ake samu a tsakanin al'uma inda rashin iya magance hakan ke jefa rayuwar dan Adam cikin hadari. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai, ministar harkokin wajen Jamus, Annelena Baebock wadda ta gabatar jawabinta ta kafar bidiyo, ta nunar da irin tasirin hadin kai tsakanin al'umma ganin yadda kowace matsala ke iya kai wa ga mutane a ko'ina suke a wannan duniya.

Shi ma firimiyan jihar North Rhine-Westphalia Hendrik Wüst, ya nunar da tasirin dan jarida inda yake cewa duk da yadda fasahar zamani ke sauya aikin ko yaushe, tilas ne a bukaci dan jarida a duniya saboda kare hakkin bil Adama da bayyana zahirin yanayin da mutane ke rayuwa. Maryan Lawan Dalhatu ta kasance 'yar jarida daga gidan rediyon Freedom da ke Kaduna a Najeriya tana cikin mahalarta taron wadda ta nuna irin tasirin muhawara da ke gudana.

0scar Martinez da shugaban DW Peter Limbourg
Hoto: Bjorn Kietzmann/DW

Shugabar da'irar birnin Bonn, Katja Dörner ta gabatar da jawabi kan muhimmancin sakar wa 'yan jarida mara, sannan ta jinjina wa Oscar Martinez dan jarida daga kasar Elsalvador wanda ya lashe kyautar gwarzon 'yan jarida da tashar DW ke bayarwa kowace shekara, saboda jajircewa wajen nuna irin yadda gwamnatin Elsalvador ta kasance mai aiki da tsageru masu dauke da makamai a fakaice yayin da take nuna cewa a tsaye take wajen magance matsalolin kasar.

Daga bisani shugaban tashar DW, Peter Limbourg ya mika kyautar gwarzon ga Oscar Martinez, kuma lokacin jawabinsa Martinez ya nunar da irin yadda ake kara samun sukurkucewar 'yancin fadin albarkacin baki a kasashen yankin tsakiya Amurka.

Tattaunawar masana da 'yan jarida zai ci gaba har zuwa ranar Talata.