DW ta yi kiran sako wakilinta.
May 22, 2017Tashar Deutsche Welle ta bukaci a sako wakilinta mai aiko da rahotanni a Burundi Antediteste Niragira wanda hukumomin tsaro a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango suka tsare tun a ranar larabar da ta gabata.
A cikin wata sanarwa tashar Deutsche Welle ta ce Jami'an leken asiri na Kwango ne suka kama dan jaridar bisa zargin leken asiri alhali ya je dauko rahotanni ne a sansanin yan gudun hijirar Burundi da ke Kavinvara kusa da iyaka da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo inda suka yi awon gaba da shi zuwa gidan yari a garin Uvira.
Sanarwar ta ce Lauyan DW ya sami ganin yanayin da dan jaridar yake ciki. Sai dai hukumomin na Kwngo sun ki yin karin bayani akan zargin leken asiri da suke yiwa wakilin na DW mai aiko da rahotanni.
Mai magana da yawun Deutsche Welle Christoph Jumpelt ya baiyana zargin leken asiri da ake yiwa wakilin na DW Antediteste Niragira da cewa zargi ne mara tushe balle makama.