1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola na yaduwa a Liberiya kamar wutar daji

September 8, 2014

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ce cutar Ebola na yaduwa a Liberiya kamar wutar daji wanda hakan ya sa ta ce ta na fargabar cutar za ta kama dubban mutane.

https://p.dw.com/p/1D8zW
Ebola Seuche Afrika Helfer
An nemi masu bada agaji da su rubanya kokarinsu don dakile cigaba da bazuwar EbolaHoto: D.Faget /AFP/Getty Images

A wata sanarwa da hukumar ta fidda ta ce motocin haya musamman ma tasi-tasi da kuma baburan da ake kabu-kabu da su, su ne babbar hanyar da a yanzu aka fi yada cutar ta Ebola a Liberiya, yayin da a hannu guda ta ce hanyoyin da ake bi wajen yakar cutar ba sa aiki kamar yadda ya dace.

Wannan ne ma ya sanya WHO din yin kira ga kungiyoyin da ke bada agaji da su ribanya irin kokarin da suke yi a kasar ta Liberiya da ma sauran sassan Afirka ta yamma inda cutar ta bulla don kawar da ita. Kimanin mutane dubu biyu ne yanzu haka cutar ta yi ajalinsu inda fiye da rabi suka rasu a Liberiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba