ECOWAS: Bukatar hadin kai wajen dawo da martabar kungiyar
February 8, 2024Shugaban hukumar zartaswar ECOWAS Omar Alieu Touray ya bayyana yanayi da kungiyar ke ciki a matsayin babban kalubale, inda ya bayyana rikicin siyasar Senegal a matsayin dambarwa mafi ta da hankali.
Wannan bayyana kaduwar ya fito fili a ne a taron da ministocin harkokin waje na kasashen yammacin Afrika suka gudanar a Abuja kan dambarwar siyasar Senegal da kuma ficewar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar ECOWAS.
Wannan yanayi da ake ciki a yammacin Afrika, lokaci ne da ya kamata kasashen su hada kawunansu wajen jaddada dimukradiyya, kamar yadda Touray, ya sanar da hakan a Abuja na tarayyar Najeriya.
Ministocin tsaro da harkokin kasashen waje na Senegal sun halarci taron, amma ba a ga fuskokin wakilan kasashen Mali da Jamhuriyar da kuma Burkina Faso ba da kungiyar ta sallama daga cikinta sakamakon juyin mulki, wanda daga bisani suka sanar da dankwafar da shahadar kasancewa a cikin kungiyar.