SiyasaAfirka
ECOWAS: Burkina Faso ta sanar da ficewa a hukumance
January 30, 2024Talla
Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun bi sahun Mali wajen mika takardar bukatar ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS a hukumance.
Tun da fari dai ma'aikatun harkokin wajen Mali da Nijar suka mika bukatar ficewa daga ECOWAS tun daga ranar 29 ga watan Janairu 2024.
Kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga kungiyar ta ECOWAS a ranar lahadin da ta gabata ta kafar talabijin a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
Matakin na kasashen uku ya biyo bayan takun-saka da ke tsakanin su da kungiyar ta ECOWAS tun bayan hambarar da gwamnatocin farar hula a lokuta daban-daban.